Setting
Surah Jonah [Yunus] in Hausa
الٓر ۚ تِلْكَ ءَايَٰتُ ٱلْكِتَٰبِ ٱلْحَكِيمِ ﴿١﴾
A. L̃.R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce.
أَكَانَ لِلنَّاسِ عَجَبًا أَنْ أَوْحَيْنَآ إِلَىٰ رَجُلٍۢ مِّنْهُمْ أَنْ أَنذِرِ ٱلنَّاسَ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنَّ لَهُمْ قَدَمَ صِدْقٍ عِندَ رَبِّهِمْ ۗ قَالَ ٱلْكَٰفِرُونَ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌۭ مُّبِينٌ ﴿٢﴾
Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, \"Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu.\"Kãfirai suka ce: \"Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne.\"
إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ فِى سِتَّةِ أَيَّامٍۢ ثُمَّ ٱسْتَوَىٰ عَلَى ٱلْعَرْشِ ۖ يُدَبِّرُ ٱلْأَمْرَ ۖ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِنۢ بَعْدِ إِذْنِهِۦ ۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمْ فَٱعْبُدُوهُ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ ﴿٣﴾
Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?
إِلَيْهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًۭا ۖ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقًّا ۚ إِنَّهُۥ يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ بِٱلْقِسْطِ ۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَهُمْ شَرَابٌۭ مِّنْ حَمِيمٍۢ وَعَذَابٌ أَلِيمٌۢ بِمَا كَانُوا۟ يَكْفُرُونَ ﴿٤﴾
zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ ٱلشَّمْسَ ضِيَآءًۭ وَٱلْقَمَرَ نُورًۭا وَقَدَّرَهُۥ مَنَازِلَ لِتَعْلَمُوا۟ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلْحِسَابَ ۚ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِٱلْحَقِّ ۚ يُفَصِّلُ ٱلْءَايَٰتِ لِقَوْمٍۢ يَعْلَمُونَ ﴿٥﴾
Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗanda suke sani.
إِنَّ فِى ٱخْتِلَٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ لَءَايَٰتٍۢ لِّقَوْمٍۢ يَتَّقُونَ ﴿٦﴾
Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin taƙawa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَآءَنَا وَرَضُوا۟ بِٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَٱطْمَأَنُّوا۟ بِهَا وَٱلَّذِينَ هُمْ عَنْ ءَايَٰتِنَا غَٰفِلُونَ ﴿٧﴾
Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mũ, kuma suka yarda da rãyuwar dũniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ãyõyinMu,
أُو۟لَٰٓئِكَ مَأْوَىٰهُمُ ٱلنَّارُ بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ ﴿٨﴾
Waɗannan matattãrarsu Jahannama ce sabõda abin da suka kasance sunã tsirfãtawa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ يَهْدِيهِمْ رَبُّهُم بِإِيمَٰنِهِمْ ۖ تَجْرِى مِن تَحْتِهِمُ ٱلْأَنْهَٰرُ فِى جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ ﴿٩﴾
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
دَعْوَىٰهُمْ فِيهَا سُبْحَٰنَكَ ٱللَّهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلَٰمٌۭ ۚ وَءَاخِرُ دَعْوَىٰهُمْ أَنِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ ﴿١٠﴾
Kiransu a cikinta, \"TsarkinKa yã Allah!\" Kuma gaisuwarsu a cikinta,\"Salãmun\", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, \"Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.\"
۞ وَلَوْ يُعَجِّلُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ ٱلشَّرَّ ٱسْتِعْجَالَهُم بِٱلْخَيْرِ لَقُضِىَ إِلَيْهِمْ أَجَلُهُمْ ۖ فَنَذَرُ ٱلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَآءَنَا فِى طُغْيَٰنِهِمْ يَعْمَهُونَ ﴿١١﴾
Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa.
وَإِذَا مَسَّ ٱلْإِنسَٰنَ ٱلضُّرُّ دَعَانَا لِجَنۢبِهِۦٓ أَوْ قَاعِدًا أَوْ قَآئِمًۭا فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُ ضُرَّهُۥ مَرَّ كَأَن لَّمْ يَدْعُنَآ إِلَىٰ ضُرٍّۢ مَّسَّهُۥ ۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلْمُسْرِفِينَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ ﴿١٢﴾
Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa.
وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا ٱلْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُوا۟ ۙ وَجَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَٰتِ وَمَا كَانُوا۟ لِيُؤْمِنُوا۟ ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْقَوْمَ ٱلْمُجْرِمِينَ ﴿١٣﴾
Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi.
ثُمَّ جَعَلْنَٰكُمْ خَلَٰٓئِفَ فِى ٱلْأَرْضِ مِنۢ بَعْدِهِمْ لِنَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ ﴿١٤﴾
Sa'an nan kuma Muka sanya ku mãsu mayẽwa a cikin ƙasa daga bãyansu, dõmin Mu ga yãya kuke aikatãwa.
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَاتُنَا بَيِّنَٰتٍۢ ۙ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَآءَنَا ٱئْتِ بِقُرْءَانٍ غَيْرِ هَٰذَآ أَوْ بَدِّلْهُ ۚ قُلْ مَا يَكُونُ لِىٓ أَنْ أُبَدِّلَهُۥ مِن تِلْقَآئِ نَفْسِىٓ ۖ إِنْ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَىَّ ۖ إِنِّىٓ أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّى عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍۢ ﴿١٥﴾
Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: \"Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi.\" Ka ce: \"Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma.\"
قُل لَّوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا تَلَوْتُهُۥ عَلَيْكُمْ وَلَآ أَدْرَىٰكُم بِهِۦ ۖ فَقَدْ لَبِثْتُ فِيكُمْ عُمُرًۭا مِّن قَبْلِهِۦٓ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ ﴿١٦﴾
Ka ce: \"Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin (fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?\"
فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ ٱفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلْمُجْرِمُونَ ﴿١٧﴾
\"Sabõda haka wãne ne mafi Zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata ãyõyinSa? Haƙĩƙa, mãsu laifibã su cin nasara!\"
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ ۚ قُلْ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِى ٱلْأَرْضِ ۚ سُبْحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ ﴿١٨﴾
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: \"Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah.\"Ka ce: \"Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi.\"
وَمَا كَانَ ٱلنَّاسُ إِلَّآ أُمَّةًۭ وَٰحِدَةًۭ فَٱخْتَلَفُوا۟ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌۭ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِىَ بَيْنَهُمْ فِيمَا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ ﴿١٩﴾
Kuma mutãne ba su kasance ba fãce al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikinsa suke sãɓã wa jũna.
وَيَقُولُونَ لَوْلَآ أُنزِلَ عَلَيْهِ ءَايَةٌۭ مِّن رَّبِّهِۦ ۖ فَقُلْ إِنَّمَا ٱلْغَيْبُ لِلَّهِ فَٱنتَظِرُوٓا۟ إِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُنتَظِرِينَ ﴿٢٠﴾
Kuma sunã cẽwa: \"Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga Ubangijinsa?\" To, ka ce: \"Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira.\"
وَإِذَآ أَذَقْنَا ٱلنَّاسَ رَحْمَةًۭ مِّنۢ بَعْدِ ضَرَّآءَ مَسَّتْهُمْ إِذَا لَهُم مَّكْرٌۭ فِىٓ ءَايَاتِنَا ۚ قُلِ ٱللَّهُ أَسْرَعُ مَكْرًا ۚ إِنَّ رُسُلَنَا يَكْتُبُونَ مَا تَمْكُرُونَ ﴿٢١﴾
Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: \"Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon) mãkirci.\" Lalle ne ManzanninMu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci.
هُوَ ٱلَّذِى يُسَيِّرُكُمْ فِى ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ ۖ حَتَّىٰٓ إِذَا كُنتُمْ فِى ٱلْفُلْكِ وَجَرَيْنَ بِهِم بِرِيحٍۢ طَيِّبَةٍۢ وَفَرِحُوا۟ بِهَا جَآءَتْهَا رِيحٌ عَاصِفٌۭ وَجَآءَهُمُ ٱلْمَوْجُ مِن كُلِّ مَكَانٍۢ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُمْ أُحِيطَ بِهِمْ ۙ دَعَوُا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ لَئِنْ أَنجَيْتَنَا مِنْ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ ﴿٢٢﴾
Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya.
فَلَمَّآ أَنجَىٰهُمْ إِذَا هُمْ يَبْغُونَ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ ۗ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَا بَغْيُكُمْ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُم ۖ مَّتَٰعَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُكُمْ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ ﴿٢٣﴾
To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa,
إِنَّمَا مَثَلُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا كَمَآءٍ أَنزَلْنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخْتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلْأَرْضِ مِمَّا يَأْكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلْأَنْعَٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلْأَرْضُ زُخْرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتْ وَظَنَّ أَهْلُهَآ أَنَّهُمْ قَٰدِرُونَ عَلَيْهَآ أَتَىٰهَآ أَمْرُنَا لَيْلًا أَوْ نَهَارًۭا فَجَعَلْنَٰهَا حَصِيدًۭا كَأَن لَّمْ تَغْنَ بِٱلْأَمْسِ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلْءَايَٰتِ لِقَوْمٍۢ يَتَفَكَّرُونَ ﴿٢٤﴾
Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni.
وَٱللَّهُ يَدْعُوٓا۟ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَٰمِ وَيَهْدِى مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٍۢ مُّسْتَقِيمٍۢ ﴿٢٥﴾
Kuma Allah Yanã kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici.
۞ لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ ٱلْحُسْنَىٰ وَزِيَادَةٌۭ ۖ وَلَا يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌۭ وَلَا ذِلَّةٌ ۚ أُو۟لَٰٓئِكَ أَصْحَٰبُ ٱلْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَٰلِدُونَ ﴿٢٦﴾
Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.
وَٱلَّذِينَ كَسَبُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ جَزَآءُ سَيِّئَةٍۭ بِمِثْلِهَا وَتَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌۭ ۖ مَّا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنْ عَاصِمٍۢ ۖ كَأَنَّمَآ أُغْشِيَتْ وُجُوهُهُمْ قِطَعًۭا مِّنَ ٱلَّيْلِ مُظْلِمًا ۚ أُو۟لَٰٓئِكَ أَصْحَٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَٰلِدُونَ ﴿٢٧﴾
Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta.
وَيَوْمَ نَحْشُرُهُمْ جَمِيعًۭا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ مَكَانَكُمْ أَنتُمْ وَشُرَكَآؤُكُمْ ۚ فَزَيَّلْنَا بَيْنَهُمْ ۖ وَقَالَ شُرَكَآؤُهُم مَّا كُنتُمْ إِيَّانَا تَعْبُدُونَ ﴿٢٨﴾
Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, \"Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku.\" Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: \"Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba.\"
فَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًۢا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ إِن كُنَّا عَنْ عِبَادَتِكُمْ لَغَٰفِلِينَ ﴿٢٩﴾
\"To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!\"
هُنَالِكَ تَبْلُوا۟ كُلُّ نَفْسٍۢ مَّآ أَسْلَفَتْ ۚ وَرُدُّوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ مَوْلَىٰهُمُ ٱلْحَقِّ ۖ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ ﴿٣٠﴾
A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu.
قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ أَمَّن يَمْلِكُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَٰرَ وَمَن يُخْرِجُ ٱلْحَىَّ مِنَ ٱلْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ ٱلْمَيِّتَ مِنَ ٱلْحَىِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلْأَمْرَ ۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُ ۚ فَقُلْ أَفَلَا تَتَّقُونَ ﴿٣١﴾
Ka ce: \"Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?\" To, zã su ce: \"Allah ne.\" To, ka ce: \"Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?\"
فَذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمُ ٱلْحَقُّ ۖ فَمَاذَا بَعْدَ ٱلْحَقِّ إِلَّا ٱلضَّلَٰلُ ۖ فَأَنَّىٰ تُصْرَفُونَ ﴿٣٢﴾
To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a bãyan gaskiya fãce ɓãta? To, yãya ake karkatar da ku?
كَذَٰلِكَ حَقَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ فَسَقُوٓا۟ أَنَّهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ ﴿٣٣﴾
Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
قُلْ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ۚ قُلِ ٱللَّهُ يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ ﴿٣٤﴾
Ka ce: \"Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?\" Ka ce: \"Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?\"
قُلْ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَهْدِىٓ إِلَى ٱلْحَقِّ ۚ قُلِ ٱللَّهُ يَهْدِى لِلْحَقِّ ۗ أَفَمَن يَهْدِىٓ إِلَى ٱلْحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لَّا يَهِدِّىٓ إِلَّآ أَن يُهْدَىٰ ۖ فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ ﴿٣٥﴾
Ka ce: \"Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?\" Ka ce: \"Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?\"
وَمَا يَتَّبِعُ أَكْثَرُهُمْ إِلَّا ظَنًّا ۚ إِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًٔا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌۢ بِمَا يَفْعَلُونَ ﴿٣٦﴾
Kuma mafi yawansu bã su biyar kõme fãce zato. Lalle ne zato bã ya wadãtar da kõme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
وَمَا كَانَ هَٰذَا ٱلْقُرْءَانُ أَن يُفْتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن تَصْدِيقَ ٱلَّذِى بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ ٱلْكِتَٰبِ لَا رَيْبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ ﴿٣٧﴾
Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.
أَمْ يَقُولُونَ ٱفْتَرَىٰهُ ۖ قُلْ فَأْتُوا۟ بِسُورَةٍۢ مِّثْلِهِۦ وَٱدْعُوا۟ مَنِ ٱسْتَطَعْتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ ﴿٣٨﴾
Kõ sunã cẽwa, \"Yã ƙirƙira shi?\" Ka ce: \"Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.\"
بَلْ كَذَّبُوا۟ بِمَا لَمْ يُحِيطُوا۟ بِعِلْمِهِۦ وَلَمَّا يَأْتِهِمْ تَأْوِيلُهُۥ ۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿٣٩﴾
Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar azzãlumai ta kasance?
وَمِنْهُم مَّن يُؤْمِنُ بِهِۦ وَمِنْهُم مَّن لَّا يُؤْمِنُ بِهِۦ ۚ وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِٱلْمُفْسِدِينَ ﴿٤٠﴾
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata.
وَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل لِّى عَمَلِى وَلَكُمْ عَمَلُكُمْ ۖ أَنتُم بَرِيٓـُٔونَ مِمَّآ أَعْمَلُ وَأَنَا۠ بَرِىٓءٌۭ مِّمَّا تَعْمَلُونَ ﴿٤١﴾
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: \"Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa.\"
وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ ۚ أَفَأَنتَ تُسْمِعُ ٱلصُّمَّ وَلَوْ كَانُوا۟ لَا يَعْقِلُونَ ﴿٤٢﴾
Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kõ dã sun kasance bã su hankalta?
وَمِنْهُم مَّن يَنظُرُ إِلَيْكَ ۚ أَفَأَنتَ تَهْدِى ٱلْعُمْىَ وَلَوْ كَانُوا۟ لَا يُبْصِرُونَ ﴿٤٣﴾
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsõkaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makãfi, kuma kõ dã sun kasance bã su gani?
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظْلِمُ ٱلنَّاسَ شَيْـًۭٔا وَلَٰكِنَّ ٱلنَّاسَ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ ﴿٤٤﴾
Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu.
وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ كَأَن لَّمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا سَاعَةًۭ مِّنَ ٱلنَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيْنَهُمْ ۚ قَدْ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِلِقَآءِ ٱللَّهِ وَمَا كَانُوا۟ مُهْتَدِينَ ﴿٤٥﴾
Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.
وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ ٱلَّذِى نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ ٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ ﴿٤٦﴾
Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa.
وَلِكُلِّ أُمَّةٍۢ رَّسُولٌۭ ۖ فَإِذَا جَآءَ رَسُولُهُمْ قُضِىَ بَيْنَهُم بِٱلْقِسْطِ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ ﴿٤٧﴾
Kuma ga kõwace al'umma akwai Manzo. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma sũ, bã a zãluntar su.
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ ﴿٤٨﴾
Kuma sunã cẽwa, \"A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance mãsu gaskiya?\"
قُل لَّآ أَمْلِكُ لِنَفْسِى ضَرًّۭا وَلَا نَفْعًا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ ۗ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۚ إِذَا جَآءَ أَجَلُهُمْ فَلَا يَسْتَـْٔخِرُونَ سَاعَةًۭ ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ ﴿٤٩﴾
Ka ce: \"Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba.\"
قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَتَىٰكُمْ عَذَابُهُۥ بَيَٰتًا أَوْ نَهَارًۭا مَّاذَا يَسْتَعْجِلُ مِنْهُ ٱلْمُجْرِمُونَ ﴿٥٠﴾
Ka ce: \"Shin, kun gani, idan azãbarSa ta zo muku da dare ko da rãna? Mẽne ne daga gare shimãsu laifi suke nẽman gaggãwarsa?\"
أَثُمَّ إِذَا مَا وَقَعَ ءَامَنتُم بِهِۦٓ ۚ ءَآلْـَٰٔنَ وَقَدْ كُنتُم بِهِۦ تَسْتَعْجِلُونَ ﴿٥١﴾
Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmãni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhãli kun kasance game da shi kunã nẽman gaggãwar aukuwarsa?
ثُمَّ قِيلَ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ذُوقُوا۟ عَذَابَ ٱلْخُلْدِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلَّا بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ ﴿٥٢﴾
Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zãlunci, \"Ku ɗanɗani azãbar dawwama! Shin, anã sãka muku fãce da abin da kuka kasance kuna aikatãwa?\"
۞ وَيَسْتَنۢبِـُٔونَكَ أَحَقٌّ هُوَ ۖ قُلْ إِى وَرَبِّىٓ إِنَّهُۥ لَحَقٌّۭ ۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعْجِزِينَ ﴿٥٣﴾
Kuma sunã tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: \"Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama mãsu buwãya ba.\"
وَلَوْ أَنَّ لِكُلِّ نَفْسٍۢ ظَلَمَتْ مَا فِى ٱلْأَرْضِ لَٱفْتَدَتْ بِهِۦ ۗ وَأَسَرُّوا۟ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ۖ وَقُضِىَ بَيْنَهُم بِٱلْقِسْطِ ۚ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ ﴿٥٤﴾
Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba.
أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ أَلَآ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّۭ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ ﴿٥٥﴾
To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ ﴿٥٦﴾
Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدْ جَآءَتْكُم مَّوْعِظَةٌۭ مِّن رَّبِّكُمْ وَشِفَآءٌۭ لِّمَا فِى ٱلصُّدُورِ وَهُدًۭى وَرَحْمَةٌۭ لِّلْمُؤْمِنِينَ ﴿٥٧﴾
Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai.
قُلْ بِفَضْلِ ٱللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا۟ هُوَ خَيْرٌۭ مِّمَّا يَجْمَعُونَ ﴿٥٨﴾
Ka ce: \"Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan.\" Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.
قُلْ أَرَءَيْتُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ لَكُم مِّن رِّزْقٍۢ فَجَعَلْتُم مِّنْهُ حَرَامًۭا وَحَلَٰلًۭا قُلْ ءَآللَّهُ أَذِنَ لَكُمْ ۖ أَمْ عَلَى ٱللَّهِ تَفْتَرُونَ ﴿٥٩﴾
Ka ce: \"Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?\" Ka ce: \"Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?\"
وَمَا ظَنُّ ٱلَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَشْكُرُونَ ﴿٦٠﴾
Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle haƙĩƙa, Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su gõdẽwa.
وَمَا تَكُونُ فِى شَأْنٍۢ وَمَا تَتْلُوا۟ مِنْهُ مِن قُرْءَانٍۢ وَلَا تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُودًا إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ ۚ وَمَا يَعْزُبُ عَن رَّبِّكَ مِن مِّثْقَالِ ذَرَّةٍۢ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فِى ٱلسَّمَآءِ وَلَآ أَصْغَرَ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكْبَرَ إِلَّا فِى كِتَٰبٍۢ مُّبِينٍ ﴿٦١﴾
Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne.
أَلَآ إِنَّ أَوْلِيَآءَ ٱللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ ﴿٦٢﴾
To, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.
ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَكَانُوا۟ يَتَّقُونَ ﴿٦٣﴾
Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.
لَهُمُ ٱلْبُشْرَىٰ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَفِى ٱلْءَاخِرَةِ ۚ لَا تَبْدِيلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ ﴿٦٤﴾
Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira. Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma,
وَلَا يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ ۘ إِنَّ ٱلْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا ۚ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ ﴿٦٥﴾
Kada maganarsu ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.
أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَن فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ ۗ وَمَا يَتَّبِعُ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُرَكَآءَ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ ﴿٦٦﴾
To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a MulkinSa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai.
هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ لِتَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبْصِرًا ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَءَايَٰتٍۢ لِّقَوْمٍۢ يَسْمَعُونَ ﴿٦٧﴾
Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji.
قَالُوا۟ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدًۭا ۗ سُبْحَٰنَهُۥ ۖ هُوَ ٱلْغَنِىُّ ۖ لَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۚ إِنْ عِندَكُم مِّن سُلْطَٰنٍۭ بِهَٰذَآ ۚ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ ﴿٦٨﴾
Suka ce: \"Allah Ya riƙi ɗa.\" Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?
قُلْ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ ﴿٦٩﴾
Ka ce: \"Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba.\"
مَتَٰعٌۭ فِى ٱلدُّنْيَا ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ ٱلْعَذَابَ ٱلشَّدِيدَ بِمَا كَانُوا۟ يَكْفُرُونَ ﴿٧٠﴾
Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
۞ وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ نُوحٍ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦ يَٰقَوْمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكُم مَّقَامِى وَتَذْكِيرِى بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَعَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلْتُ فَأَجْمِعُوٓا۟ أَمْرَكُمْ وَشُرَكَآءَكُمْ ثُمَّ لَا يَكُنْ أَمْرُكُمْ عَلَيْكُمْ غُمَّةًۭ ثُمَّ ٱقْضُوٓا۟ إِلَىَّ وَلَا تُنظِرُونِ ﴿٧١﴾
Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, \"Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri.\"
فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَمَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْمُسْلِمِينَ ﴿٧٢﴾
\"Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa.\"
فَكَذَّبُوهُ فَنَجَّيْنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِى ٱلْفُلْكِ وَجَعَلْنَٰهُمْ خَلَٰٓئِفَ وَأَغْرَقْنَا ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَٰتِنَا ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلْمُنذَرِينَ ﴿٧٣﴾
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
ثُمَّ بَعَثْنَا مِنۢ بَعْدِهِۦ رُسُلًا إِلَىٰ قَوْمِهِمْ فَجَآءُوهُم بِٱلْبَيِّنَٰتِ فَمَا كَانُوا۟ لِيُؤْمِنُوا۟ بِمَا كَذَّبُوا۟ بِهِۦ مِن قَبْلُ ۚ كَذَٰلِكَ نَطْبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلْمُعْتَدِينَ ﴿٧٤﴾
Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi.
ثُمَّ بَعَثْنَا مِنۢ بَعْدِهِم مُّوسَىٰ وَهَٰرُونَ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦ بِـَٔايَٰتِنَا فَٱسْتَكْبَرُوا۟ وَكَانُوا۟ قَوْمًۭا مُّجْرِمِينَ ﴿٧٥﴾
Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi.
فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوٓا۟ إِنَّ هَٰذَا لَسِحْرٌۭ مُّبِينٌۭ ﴿٧٦﴾
Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: \"Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne.\"
قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلْحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمْ ۖ أَسِحْرٌ هَٰذَا وَلَا يُفْلِحُ ٱلسَّٰحِرُونَ ﴿٧٧﴾
Mũsã ya ce: \" Shin, kunã cẽwa ga gaskiya a lõkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bã ya cin nasara.\"
قَالُوٓا۟ أَجِئْتَنَا لِتَلْفِتَنَا عَمَّا وَجَدْنَا عَلَيْهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلْكِبْرِيَآءُ فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا نَحْنُ لَكُمَا بِمُؤْمِنِينَ ﴿٧٨﴾
Suka ce: \"Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku.\"
وَقَالَ فِرْعَوْنُ ٱئْتُونِى بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٍۢ ﴿٧٩﴾
Kuma Fir'auna ya ce: \"Ku zo mini da dukan masihirci, masani.\"
فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلْقُوا۟ مَآ أَنتُم مُّلْقُونَ ﴿٨٠﴾
To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,\"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa.\"
فَلَمَّآ أَلْقَوْا۟ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئْتُم بِهِ ٱلسِّحْرُ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبْطِلُهُۥٓ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصْلِحُ عَمَلَ ٱلْمُفْسِدِينَ ﴿٨١﴾
To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: \"Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata.
وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلْحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْمُجْرِمُونَ ﴿٨٢﴾
\"Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi.\"
فَمَآ ءَامَنَ لِمُوسَىٰٓ إِلَّا ذُرِّيَّةٌۭ مِّن قَوْمِهِۦ عَلَىٰ خَوْفٍۢ مِّن فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِمْ أَن يَفْتِنَهُمْ ۚ وَإِنَّ فِرْعَوْنَ لَعَالٍۢ فِى ٱلْأَرْضِ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلْمُسْرِفِينَ ﴿٨٣﴾
Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna.
وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰقَوْمِ إِن كُنتُمْ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ فَعَلَيْهِ تَوَكَّلُوٓا۟ إِن كُنتُم مُّسْلِمِينَ ﴿٨٤﴾
Kuma Mũsã ya ce: \"Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi.\"
فَقَالُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلْنَا رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا فِتْنَةًۭ لِّلْقَوْمِ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿٨٥﴾
Sai suka ce: \"Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne azzãlumai.
وَنَجِّنَا بِرَحْمَتِكَ مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلْكَٰفِرِينَ ﴿٨٦﴾
\"Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai.\"
وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوْمِكُمَا بِمِصْرَ بُيُوتًۭا وَٱجْعَلُوا۟ بُيُوتَكُمْ قِبْلَةًۭ وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿٨٧﴾
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni.
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبَّنَآ إِنَّكَ ءَاتَيْتَ فِرْعَوْنَ وَمَلَأَهُۥ زِينَةًۭ وَأَمْوَٰلًۭا فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّوا۟ عَن سَبِيلِكَ ۖ رَبَّنَا ٱطْمِسْ عَلَىٰٓ أَمْوَٰلِهِمْ وَٱشْدُدْ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُوا۟ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ ﴿٨٨﴾
Sai MũSã ya ce: \"Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi.\"
قَالَ قَدْ أُجِيبَت دَّعْوَتُكُمَا فَٱسْتَقِيمَا وَلَا تَتَّبِعَآنِّ سَبِيلَ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ ﴿٨٩﴾
(Allah) Yã ce: \"Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba.\"
۞ وَجَٰوَزْنَا بِبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱلْبَحْرَ فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ وَجُنُودُهُۥ بَغْيًۭا وَعَدْوًا ۖ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَدْرَكَهُ ٱلْغَرَقُ قَالَ ءَامَنتُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱلَّذِىٓ ءَامَنَتْ بِهِۦ بَنُوٓا۟ إِسْرَٰٓءِيلَ وَأَنَا۠ مِنَ ٱلْمُسْلِمِينَ ﴿٩٠﴾
Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: \"Nã yi ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi.\"
ءَآلْـَٰٔنَ وَقَدْ عَصَيْتَ قَبْلُ وَكُنتَ مِنَ ٱلْمُفْسِدِينَ ﴿٩١﴾
Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna?
فَٱلْيَوْمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنْ خَلْفَكَ ءَايَةًۭ ۚ وَإِنَّ كَثِيرًۭا مِّنَ ٱلنَّاسِ عَنْ ءَايَٰتِنَا لَغَٰفِلُونَ ﴿٩٢﴾
To, a yau Munã kuɓutar da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.
وَلَقَدْ بَوَّأْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ مُبَوَّأَ صِدْقٍۢ وَرَزَقْنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ فَمَا ٱخْتَلَفُوا۟ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلْعِلْمُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِى بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ ﴿٩٣﴾
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.
فَإِن كُنتَ فِى شَكٍّۢ مِّمَّآ أَنزَلْنَآ إِلَيْكَ فَسْـَٔلِ ٱلَّذِينَ يَقْرَءُونَ ٱلْكِتَٰبَ مِن قَبْلِكَ ۚ لَقَدْ جَآءَكَ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُمْتَرِينَ ﴿٩٤﴾
To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littãfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tã jẽ maka daga Ubangijinka dõmin haka kada ka kasance daga mãsu kõkanto.
وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَتَكُونَ مِنَ ٱلْخَٰسِرِينَ ﴿٩٥﴾
Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatãwa game da ãyõyin Allah, har ka kasance daga mãsu hasãra.
إِنَّ ٱلَّذِينَ حَقَّتْ عَلَيْهِمْ كَلِمَتُ رَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ ﴿٩٦﴾
Lalle ne waɗanda kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, bã zã su yi ĩmãni ba.
وَلَوْ جَآءَتْهُمْ كُلُّ ءَايَةٍ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ ﴿٩٧﴾
Kuma kõ dã kõwace ãyã ta jẽ musu, sai sun ga azãba mai raɗaɗi.
فَلَوْلَا كَانَتْ قَرْيَةٌ ءَامَنَتْ فَنَفَعَهَآ إِيمَٰنُهَآ إِلَّا قَوْمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُوا۟ كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ ٱلْخِزْىِ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَمَتَّعْنَٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍۢ ﴿٩٨﴾
To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.
وَلَوْ شَآءَ رَبُّكَ لَءَامَنَ مَن فِى ٱلْأَرْضِ كُلُّهُمْ جَمِيعًا ۚ أَفَأَنتَ تُكْرِهُ ٱلنَّاسَ حَتَّىٰ يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ ﴿٩٩﴾
Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni?
وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَن تُؤْمِنَ إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ وَيَجْعَلُ ٱلرِّجْسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ ﴿١٠٠﴾
Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma (Allah) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗanda bã su yin hankali.
قُلِ ٱنظُرُوا۟ مَاذَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَمَا تُغْنِى ٱلْءَايَٰتُ وَٱلنُّذُرُ عَن قَوْمٍۢ لَّا يُؤْمِنُونَ ﴿١٠١﴾
Ka ce: \"Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa.\"Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni.
فَهَلْ يَنتَظِرُونَ إِلَّا مِثْلَ أَيَّامِ ٱلَّذِينَ خَلَوْا۟ مِن قَبْلِهِمْ ۚ قُلْ فَٱنتَظِرُوٓا۟ إِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُنتَظِرِينَ ﴿١٠٢﴾
To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãninsu? Ka ce: \"Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira.\"
ثُمَّ نُنَجِّى رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ۚ كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنجِ ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿١٠٣﴾
Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni.
قُلْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمْ فِى شَكٍّۢ مِّن دِينِى فَلَآ أَعْبُدُ ٱلَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِنْ أَعْبُدُ ٱللَّهَ ٱلَّذِى يَتَوَفَّىٰكُمْ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿١٠٤﴾
Ka ce: \"Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa, waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni.\"
وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًۭا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ ﴿١٠٥﴾
\"Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka.
وَلَا تَدْعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ ۖ فَإِن فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًۭا مِّنَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿١٠٦﴾
\"Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci.\"
وَإِن يَمْسَسْكَ ٱللَّهُ بِضُرٍّۢ فَلَا كَاشِفَ لَهُۥٓ إِلَّا هُوَ ۖ وَإِن يُرِدْكَ بِخَيْرٍۢ فَلَا رَآدَّ لِفَضْلِهِۦ ۚ يُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ ۚ وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ ﴿١٠٧﴾
Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
قُلْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدْ جَآءَكُمُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ ۖ فَمَنِ ٱهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِى لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۖ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيْكُم بِوَكِيلٍۢ ﴿١٠٨﴾
Ka ce: \"Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba.\"
وَٱتَّبِعْ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيْكَ وَٱصْبِرْ حَتَّىٰ يَحْكُمَ ٱللَّهُ ۚ وَهُوَ خَيْرُ ٱلْحَٰكِمِينَ ﴿١٠٩﴾
Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci.