Setting
Surah The Disbelievers [Al-Kafiroon] in Hausa
Surah The Disbelievers [Al-Kafiroon] Ayah 6 Location Maccah Number 109
قُلْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلْكَٰفِرُونَ ﴿١﴾
Ka ce: \"Ya kũ kãfirai!\"
لَآ أَعْبُدُ مَا تَعْبُدُونَ ﴿٢﴾
\"Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba.\"
وَلَآ أَنتُمْ عَٰبِدُونَ مَآ أَعْبُدُ ﴿٣﴾
\"Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba.\"
وَلَآ أَنَا۠ عَابِدٌۭ مَّا عَبَدتُّمْ ﴿٤﴾
\"Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba.\"
وَلَآ أَنتُمْ عَٰبِدُونَ مَآ أَعْبُدُ ﴿٥﴾
\"Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake bautã wa ba.\"
لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِىَ دِينِ ﴿٦﴾
\"Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni.\"