Setting
Surah The Ranks [As-Saff] in Hausa
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۖ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ ﴿١﴾
Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفْعَلُونَ ﴿٢﴾
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa?
كَبُرَ مَقْتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُوا۟ مَا لَا تَفْعَلُونَ ﴿٣﴾
Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa.
إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلَّذِينَ يُقَٰتِلُونَ فِى سَبِيلِهِۦ صَفًّۭا كَأَنَّهُم بُنْيَٰنٌۭ مَّرْصُوصٌۭ ﴿٤﴾
Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna.
وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِۦ يَٰقَوْمِ لِمَ تُؤْذُونَنِى وَقَد تَّعْلَمُونَ أَنِّى رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيْكُمْ ۖ فَلَمَّا زَاغُوٓا۟ أَزَاغَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمْ ۚ وَٱللَّهُ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْفَٰسِقِينَ ﴿٥﴾
Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: \"Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Al1ah ne zuwa gare ku?\" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai.
وَإِذْ قَالَ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ يَٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ إِنِّى رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيْكُم مُّصَدِّقًۭا لِّمَا بَيْنَ يَدَىَّ مِنَ ٱلتَّوْرَىٰةِ وَمُبَشِّرًۢا بِرَسُولٍۢ يَأْتِى مِنۢ بَعْدِى ٱسْمُهُۥٓ أَحْمَدُ ۖ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلْبَيِّنَٰتِ قَالُوا۟ هَٰذَا سِحْرٌۭ مُّبِينٌۭ ﴿٦﴾
Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: \"Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, SũnasaAhmad (Mashãyabo).\" To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: \"Wannan sihiri ne, bayyananne.\"
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ ٱفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ وَهُوَ يُدْعَىٰٓ إِلَى ٱلْإِسْلَٰمِ ۚ وَٱللَّهُ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿٧﴾
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
يُرِيدُونَ لِيُطْفِـُٔوا۟ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفْوَٰهِهِمْ وَٱللَّهُ مُتِمُّ نُورِهِۦ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْكَٰفِرُونَ ﴿٨﴾
Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu alhãli kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne, kuma kõ da kãfirai sun ƙi.
هُوَ ٱلَّذِىٓ أَرْسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلْهُدَىٰ وَدِينِ ٱلْحَقِّ لِيُظْهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْمُشْرِكُونَ ﴿٩﴾
Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰ تِجَٰرَةٍۢ تُنجِيكُم مِّنْ عَذَابٍ أَلِيمٍۢ ﴿١٠﴾
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi?
تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُجَٰهِدُونَ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمْوَٰلِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌۭ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ ﴿١١﴾
Ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani.
يَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَيُدْخِلْكُمْ جَنَّٰتٍۢ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةًۭ فِى جَنَّٰتِ عَدْنٍۢ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ ﴿١٢﴾
Sai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma.
وَأُخْرَىٰ تُحِبُّونَهَا ۖ نَصْرٌۭ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَتْحٌۭ قَرِيبٌۭ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿١٣﴾
Da wata (falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُونُوٓا۟ أَنصَارَ ٱللَّهِ كَمَا قَالَ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ لِلْحَوَارِيِّۦنَ مَنْ أَنصَارِىٓ إِلَى ٱللَّهِ ۖ قَالَ ٱلْحَوَارِيُّونَ نَحْنُ أَنصَارُ ٱللَّهِ ۖ فَـَٔامَنَت طَّآئِفَةٌۭ مِّنۢ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ وَكَفَرَت طَّآئِفَةٌۭ ۖ فَأَيَّدْنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ عَلَىٰ عَدُوِّهِمْ فَأَصْبَحُوا۟ ظَٰهِرِينَ ﴿١٤﴾
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, \"Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?\" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya.